A bayanin da rundunar 'yan sandan ta yi wa manema labarai ta tabbatar da cewa, an kame mutanen ne alokacin da suke dauke da makudan kudade a wasu ungunni a cikin Kano, inda suke karbar katukan zabe daga hannun mutane, suna ba su kudi.
Bayanin ya ce wannan yana daga cikin manyan laifuka na zabe, wanda hukumar ta 'yan sanda a jahar Kano take daukar kwararn matakai a kansa, tare da shan alwashiun ba za ta saurara wa kowa ba matukar aka same shi da laifi irin wannan, daga masu sayen har zuwa masu sayarwa.
'Yan sanda sun kame mutanen ne a lokacin da jama'a suke hankoron halaka su, bayan da aka same su suna sayen katukan zabe, abin da jama'a ke danganta shi da wani yunkuri na shirya magudin zaben da za a sake gudanarwa a wasu mazabu a cikin jahar, duk kuwa da cewa 'yan sandan ba su yi bayani kan mutanen da suka kama ba da kuma bangarorin siyasar da suka sanya su yin hakan.